- Ana kishin kishin din zai sauya sheka, Mallam Nasir El-Rufa'i ya sauka a jihar Borno domin gudanar da wani muhimmin al'amari
- Wani hadimi ga tsohon gwamnan ya tabbatar da faruwar lamarin ta wata sanarwa a ranar Lahadi, 14 ga Afrilu tare da bayyana dalili
- ‘Yan Najeriya a soshiyal midiya sun yi martani dangane da faruwar lamarin, wasu na ganin cewa akwai shirin da El-Rufai yake yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Borno - Yayin da ake sukar gwamnatinsa da kuma jita-jitar sauya sheka, Mallam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya dura jihar Borno a halin yanzu.

Me yasa El-Rufai yaje jihar Borno?

Kara karanta wannan
Ana daf da zabe, tsohon Sanata da ɗan Majalisa sun watsar da PDP, sun koma APC
El-Rufai dai ya je jihar ne domin wata muhimmiyar ganawa da gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muyiwa Adekeye, hadimin El-Rufai kan harkokin yada labarai ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, 14 ga Afrilu, 2024.
Ya yi nuni da cewa tsohon gwamnan zai yi jawabi ne a taron karawa juna sani na gwamnatin jihar Borno.
Adekeye ya wallafa cewa:
"Mai girma Farfesa Babagana Umara Zulum ya tarbi Malam Nasir @elrufai a Maiduguri. Malam @elrufai zai yi jawabi ne a wani taron karawa juna sani na gwamnatin jihar Borno."'Yan Najeriya sun magantu ziyarar El-Rufai
Legit.ng ta dauko wasu ra'ayoyi na jama'a dangane da zuwan El-Rufai Borno:
@martinokorowu ya ce:

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun farmaki tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, sun tafka ɓarna a jihar Arewa
"Abu ne mai kyau."@AdamawaLas79384 ya ce:
"Malam yana shirya wani babban abu."@Zarmaomar ya ce:
"Shugaban tarayyar Najeriya mai jiran gado."@ibroayo ya ce:
"Mutum mai daraja ne kawai ke iya yin magana a taron karawa juna sani ga mutane masu daraja."@AuwalBalabakori:
"Har yanzu mutumin yana kan ganiyarsa, Allah ya kara yi wa rayuwa albarka yallabai."El-Rufai ya shirya fada da Tinubu?
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya shirya yin fada da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
KAmar yadda rahotanni suka bayyana, za a yi wannan fadan ne a gaban kotu bayan da El-Rufai ya shirya wanke kansa daga zargin da ake na cewa shi hatsari ne ga tsaron Najeriya.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbYR4hJJmmKeZXaC2tLTIp2SkoaOdtq95w6KlZrKRnnq0rdSymGarmJq4onnEpWSrrZaWtm7FwGaxorGRp7CqecawmKamkaN6o7vRp6Zo